Tinubu Ya Isa jihar Filato Don Ta’aziyya Kan Kisan da 'yan bindiga Suka yi Garin Jos.

Tinubu Ya Isa jihar Filato Don Ta’aziyya Kan Kisan da 'yan bindiga Suka yi Garin Jos.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Jos na jihar Filato, a wani ziyarar ta’aziyya kan hare-haren kisan kai da suka faru kwanan nan a jihar.

Ziyarar ta biyo bayan jerin hare-hare da aka samu a wasu yankuna na Jos, musamman a Angwan Rukuba, inda aka kashe mutane akalla 27 tare da raunata wasu da dama.

Tinubu ya dage tafiyarsa da aka shirya zuwa jihar Ogun domin ba da muhimmanci ga ziyarar ta’aziyya da nuna alhini ga gwamnatin da mutanen Filato kan wannan al’amari mai tayar da hankali.

Kafin ziyarar, shugaban ƙasa ya gana da gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda aka yi masa cikakken bayani kan halin tsaro da kuma matakan da ake ɗauka don tabbatar da zaman lafiya.

A halin yanzu, an ƙara tsaro a jihar, inda Shugaban ‘Yan Sanda na Ƙasa ya umarci a tura karin jami’an rundunar Mobile Police da tawagogin yaki domin hana sake barkewar tashin hankali da tabbatar da tsari.

Ziyarar ta’aziyya na daga cikin kokarin Gwamnatin Tarayya wajen magance matsalolin tsaro a jihar Filato da kuma hana faruwar irin wannan mummunan al’amari nan gaba.

News Translation in English Language.

Tinubu Visits Jos to Condole Victims of Plateau Killings.

President Bola Ahmed Tinubu has arrived in Jos, Plateau State, on a condolence visit following recent deadly attacks in the region.

The visit follows a series of violent incidents in parts of Jos, particularly in the Angwan Rukuba area, where at least 27 people were killed and several others injured.

Tinubu postponed a planned trip to Ogun State to prioritize this visit, expressing sympathy to the Plateau State government and residents over the tragic events.

Before traveling to Jos, the President met with Plateau State Governor Caleb Mutfwang at the Presidential Villa in Abuja, where he received detailed briefings on the security situation and ongoing efforts to restore peace.

Security has been reinforced across the state, with the Inspector-General of Police ordering the deployment of additional Mobile Police units and tactical teams to prevent further violence and maintain order.

The condolence visit forms part of the Federal Government’s broader efforts to address security challenges in Plateau State and prevent similar attacks in the future.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: