Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile wani harin da ake zargin mayakan ISWAP sun kai a Jihar Yobe, inda suka kashe ’yan ta’adda 24 a wata kazamar arangama.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa maharan sun kaddamar da harin ne daga bangarori da dama a cikin dare, inda suka yi kokarin mamaye sansanin sojojin.
Sai dai sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa tare da amfani da ingantaccen dabarun yaki da kuma karfin makamai, wanda ya tilasta wa maharan ja da baya bayan sun fuskanci mummunar asara.
Hukumomin soji sun tabbatar da cewa an kuma kwato makamai da alburusai da ’yan ta’addan suka bari yayin gudu. An kuma tura karin dakarun soji da tallafin jiragen sama domin tabbatar da tsaro a yankin.
A halin yanzu, sojoji na ci gaba da gudanar da sintiri a kauyukan da ke kusa domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron yankin baki daya.

0 Comments:
Post a Comment