Shugabanni ƙasashen yankin Gulf sun Gudanar da taro a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya, karkashin jagorancin Yarima mai jiran gado na Saudi Arabiya, Mohammed bin Salman.
Taron ya hada shugabanni da wakilai daga Saudi Arabiya da Qatar da Kuwait da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman.
Rahotanni sun bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro a yankin da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki da Ƙasar Iran ta kaiwa Sansanonin sojin Amurka a yankin, da kuma yadda kasashen Gulf din za su hada kai wajen tunkarar rikicin da ke kara fadada.
Haka kuma, an duba wasu manyan abubuwan da ke faruwa a duniya da suka shafi rikicin, tare da neman hanyoyin diflomasiyya da tsaro domin rage tashin hankali a yankin.
Taron ya gudana ne a daidai lokacin da yankin ke fuskantar rashin tabbas na tsaro, inda kasashen Gulf ke kara damuwa kan tasirin rikicin a harkokin makamashi da hanyoyin jigilar kayayyaki.
Shugabannin sun jaddada bukatar hadin kai da kara karfafa zumunci tsakanin kasashen domin shawo kan wannan matsalar tsaro da ake ganin ta fi kowace girma a ‘yan shekarun nan.

0 $type={blogger}:
Post a Comment