An ayyana Romuald Wadagni, Ministan Kuɗi na ƙasar Benin, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa, bayan samun gagarumar nasara da fiye da kashi 94% na kuri’u, a cewar sakamakon wucin-gadi da hukumar zaɓe ta sanar.
An gudanar da zaben ne a ranar 12 ga Afrilu, 2026, inda Wadagni—wanda shi ne ɗan takarar kawancen jam’iyya mai mulki kuma na hannun daman shugaban ƙasa mai barin gado Patrice Talon—ya doke abokin hamayya Paul Hounkpè, wanda ya samu kusan kashi 6% na kuri’un.
Hukumar zaɓe ta bayyana cewa an samu fitowar masu kaɗa ƙuri’a kusan kashi 58.7%, bayan kammala kirga kusan dukkanin rumfunan zabe a fadin ƙasar.
Wadagni, tsohon jami’in kamfanin Deloitte kuma Ministan Kuɗi na dogon lokaci, an dade ana ganin shi a matsayin wanda zai gaji Shugaba Talon, wanda ke kammala wa’adinsa bisa doka.
Shugabannin ‘yan adawa sun amince da shan kaye, yayin da masu sa ido daga yankin suka bayyana cewa an gudanar da zaben cikin lumana, duk da cewa masu sukar lamari sun taɓa nuna damuwa kan ƙarancin gasa ta siyasa a ƙasar.
Wannan sakamako na nuna babban sauyin siyasa a Benin, inda ake sa ran Wadagni zai ci gaba da manufofin tattalin arzikin gwamnatin da ta shude tare da fuskantar ƙalubalen tsaro a arewacin ƙasar.

0 Comments:
Post a Comment