Matatar man fatur na Dangote Ta Kara Farashin mai Zuwa ₦1,275.

Matatar man fatur na Dangote Ta Kara Farashin mai Zuwa ₦1,275.

Matatar mai ta Dangote ta ƙara farashin man fetur zuwa ₦1,275 akan kowace lita, yayin da farashin diesel ya koma ₦1,950 kan kowace lita a sabon sauyin farashin da ta yi.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin kusan ₦75 kan litar man fetur, da kuma kusan ₦200 kan litar man diesel idan aka kwatanta da farashin baya.

Masana harkar mai sun danganta wannan sauyi da tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya da sauyin darajar canjin kuɗi, da kuma ƙarin kuɗin gudanar da aiki a masana’antar mai.

Ana fargabar wannan ƙarin zai shafi harkokin sufuri da kasuwanci da farashin kayayyaki a kasuwa, domin mai na taka muhimmiyar rawa wajen ƙayyade farashin kayan masarufi.

Masu nazari sun yi gargadi cewa idan rashin tabbas a kasuwar mai ta duniya ya ci gaba, za a iya samun ƙarin sauye-sauyen farashi nan gaba.

0 $type={blogger}: