Iran ta yi gargadin yiwuwa Ta Kaddamar da Hare-haren Martani Idan Isra’ila Ta Ci Gaba da Keta Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta.

Iran ta yi gargadin yiwuwa Ta Kaddamar da Hare-haren Martani Idan Isra’ila Ta Ci Gaba da Keta Yarjejeniyar Tsagaita bude Wuta.

Jami’an gwamnatin Iran sun bayyana cewa ƙasar na iya komawa Kai Hare-haren Martani akan Israi'la da Amurka a kowane lokaci, idan har Isra’ila ta ci gaba da abin da suka kira keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.

Wannan gargadi ya zo ne yayin da ake ci gaba da samun sabani tsakanin bangarorin biyu kan yadda ake fassara yarjejeniyar. 
Iran na zargin Isra’ila da ci gaba da kai hare-hare, musamman a ƙasar Lebanon, wanda ta ce ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Sai dai Isra’ila ta musanta zargin, inda ta ce hare-haren da take kaiwa kan kungiyar Hezbollah a Lebanon ba su cikin sharuddan yarjejeniyar, don haka ba ta keta dokar tsagaita bude wutar ba.

Rahotanni daga kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun nuna cewa duk da yarjejeniyar, har yanzu ana ci gaba da kai hare-haren soji a wasu yankuna, lamarin da ke nuna cewa tsagaita bude wutar na da rauni kuma na iya rushewa a kowane lokaci.

Masana harkokin tsaro sun yi gargadin cewa wannan rikici na iya kara kamari cikin gaggawa idan bangarorin suka kasa cimma daidaito kan aiwatar da yarjejeniyar.

Duk da kasancewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, rikicin Iran da Isra’ila na ci gaba da zama cikin yanayi mai hadari, tare da yiwuwar barkewar sabon rikici a kowanne lokaci.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: