Yakin Amurka Da Isra’ila Kan iran Zai Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba - Donald Trump.

Yakin Amurka Da Isra’ila Kan iran Zai Ƙare Nan Ba Da Jimawa Ba - Donald Trump.

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yakin da ƙasarsa tare da Israel suke yi da Iran zai iya ƙarewa cikin kankanin lokaci.

Trump ya yi wannan furuci ne yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce rundunonin Amurka da Isra’ila suna samun gagarumar nasara a hare-haren da suke kaiwa kan muhimman wuraren sojin Iran. Ya ce hare-haren sun lalata wasu manyan cibiyoyin tsaron Iran, wanda hakan ya sa yakin yake kusa da ƙarewa.

A cewarsa, rundunonin haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila sun samu ci gaba mai yawa wajen cimma burin da suka sanya a gaba, yana mai cewa: “Muna kan gaba sosai wajen kammala wannan aiki, kuma ina ganin yakin zai ƙare nan ba da jimawa ba.”

Trump ya kuma yi hasashen cewa farashin man fetur a duniya zai sauka, bayan da ya tashi matuƙa sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan rikicin da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ƙara tsananta tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai farmaki kan wasu wuraren soji a Iran, lamarin da ya jawo mayar da martani daga Iran. 
Duk da haka, Trump ya jaddada cewa hare-haren na da nufin takaita ƙarfin sojin Iran ne, kuma ana sa ran rikicin zai zo ƙarshe cikin gaggawa.

Masana harkokin siyasa sun ce duk da irin wannan hasashe daga shugaban Amurka, har yanzu akwai damuwa kan yadda rikicin zai iya shafar tsaron yankin da kuma tattalin arzikin duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form