Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC mai mulki.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na siyasa a jihar da kuma nazari kan halin da jam’iyyar PDP ke ciki a matakin jiha da na kasa.
A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai, Nuhu Anka, ya fitar, ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da rashin jituwa a PDP sun zama babban kalubale ga tafiyar da gwamnati da kuma kokarin samar da ci gaba a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya yanke shawarar komawa APC ne domin samar da hadin kai da kuma karfafa alaka da gwamnatin tarayya, domin samun sauki wajen aiwatar da manufofin da za su kawo ci gaba da inganta tsaro a jihar.
Haka kuma, mataimakin gwamnan jihar, Mani Malam Mummuni, ya tabbatar da sauya shekar a madadin gwamnan tare da wasu manyan jami’an gwamnati na jihar.
Masu nazarin siyasa na ganin cewa wannan sauya sheka na iya kara karfin jam’iyyar APC a fagen siyasar kasar nan, musamman yayin da ake tunkarar zabukan shekarar 2027.
News Translation in English Language.
Zamfara Governor Dauda Lawal Defects from Peoples Democratic Party to All Progressives Congress.
The Governor of Zamfara State, Dauda Lawal, has announced his defection from the Peoples Democratic Party (PDP) to the All Progressives Congress (APC).
According to reports, the governor made the decision after consultations with political stakeholders in the state and a review of the situation within the PDP at both the state and national levels.
In a statement issued by the governor’s media aide, Nuhu Anka, it was explained that the persistent internal crises and disagreements within the PDP had become a major challenge to governance and the administration’s efforts to deliver development in the state.
The statement added that the governor decided to join the APC in order to promote unity and strengthen cooperation with the federal government, particularly to enhance development initiatives and improve security in the state.
Meanwhile, the Deputy Governor of the state, Mani Malam Mummuni, also confirmed the defection on behalf of the governor alongside other top government officials.
Political analysts believe the move could further strengthen the APC’s political influence in Nigeria as the country gradually approaches the 2027 general elections.
Tags
Labarai
