Yadda Jama'a Suka yi wa wani mutum dukan tsiya kan zargin satan Mota a ƙasar Afirka ta Kudu.

Yadda Jama'a Suka yi wa wani mutum dukan tsiya kan zargin satan Mota a ƙasar Afirka ta Kudu.

An ruwaito cewa wasu fusatattun jama’a sun yi wa wani mutum dukan tsiya bayan sun kama shi bisa zargin shirin kwace mota.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a kan titin Winnie Mandela Drive da ke kan hanyar zuwa Diepsloot a ƙasar Afrika ta kudu a ranar Laraba, 11 ga Maris, 2026.

A cewar majiyoyi, mazauna yankin ne suka tare mutumin bayan sun zarge shi da yunƙurin kwace wata mota, lamarin da ya janyo rikici tare da kai shi ga shan dukan tsiya da jama’a suka yi masa.

Sai dai hukumomi sun ci gaba da kira ga al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu. Inda suka jaddada cewa ya kamata duk wanda ya ga ko ya yi zargin wani da laifi ya kai rahoto ga ‘yan sanda domin a bi hanyoyin shari’a da doka ta tanada wajen magance irin waɗannan lamurra.

News Translation in English Language.

Suspected Car Hijacker Beaten by Public in South Africa.

A man suspected of planning a car hijacking was reportedly beaten by members of the public after being caught in the act.

The incident occurred along Winnie Mandela Drive en route to Diepsloot in South Africa on Wednesday, March 11, 2026.

According to sources, local residents confronted the man after accusing him of attempting to hijack a vehicle, which escalated into a physical assault.

Authorities continue to urge residents not to take the law into their own hands, emphasizing that suspected criminal activity should be reported to the police so it can be handled through proper legal channels.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form