Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3, tare da Kwace makamai a Dajin Sokoto.


Sojojin Najeriya, karkashin Operation FANSAN YAMMA na, sun kashe ‘yan ta’adda uku a yayin wani farmaki na fatattakar mayaka a Dajin Kadam, dake ƙaramar hukumar Tangaza a Jihar Sokoto.

A cewar kakakin rundunar sojin Bataliya na 7, sun yi nasarar kaiwa ga mayakan bayan samun bayanan sirri masu inganci cewa akwai sama da mayaka 100 a dajin suna shirin kai hare‑hare da satar mutane. 
An yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan ta’addan, inda aka kashe uku, yayin da wasu suka tsere cikin daji.

A yayin farmakin da aka gudanar bayan fafatawar, an samu makamai da kayan maye, wanda suka hada da:

Babban bindiga PKT guda 1

Bindugu AK‑47 guda 2

Kwanson harsasai PKT guda 350

Kwanson harsasai 7.62mm guda 111

Magazines guda 3

Radiyon sadarwa guda 2

Babura guda 3

Wayar hannu guda 1

Rundunar sojoji ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin leƙen mayaka da kamo sauran ‘yan ta’adda don tabbatar da tsaro a yankin da dajin ke ciki. 
Haka zalika, sojoji sun bayyana cewa irin wadannan ayyuka na bayanan sirri da hadin gwiwar tsaro suna rage karfin ‘yan ta’adda a Arewacin Najeriya, musamman Sokoto.

News Translation in English Language.

Troops Kill 3 Terrorists, Recover Weapons in Sokoto Forest.

Nigerian troops, under Operation FANSAN YAMMA of the Joint Task Force North West, have killed three terrorists during a clearance operation in Kadam Forest, Tangaza, Sokoto State.

According to military sources, soldiers from the Chief of Army Staff Special Intervention Battalion 7 and the 8 Division Strike Team successfully intercepted the militants after receiving credible intelligence that more than 100 fighters were gathering in the forest to plan attacks and kidnappings. A gun battle ensued, resulting in three deaths, while others reportedly fled deeper into the forest.

During a post-battle search, troops recovered weapons and military equipment, including:

1 PKT machine gun

2 AK‑47 rifles

350 rounds of PKT ammunition

111 rounds of 7.62mm ammunition

3 magazines

2 communication radios

3 motorcycles

1 mobile phone

The military stated that follow-up operations are ongoing to track down fleeing militants and recover additional weapons to ensure security in the area. They emphasized that such intelligence-driven and joint security operations continue to degrade terrorist capabilities in Northwestern Nigeria, particularly Sokoto State.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form