Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da rike kyawawan dabi’u da darussan da suka koya a watan Ramadan.
Sarkin ya bayyana hakan ne bayan jagorantar sallar Eid al-Fitr a filin Idi na Kofar Mata da ke Kano, inda dubban masu ibada suka taru domin gudanar da ibadar cikin kwanciyar hankali.
A cikin hudubarsa, ya jaddada cewa darussan Ramadan ba su takaitu ga lokacin azumi kadai ba, yana mai kira ga Musulmi da su ci gaba da rungumar halaye nagari kamar tausayi, hakuri da kuma taimakon marasa galihu.
Ya kuma bukaci al’umma da su kara kaimi wajen taimakon masu bukata, musamman marayu da marasa karfi, domin karfafa zumunci da hadin kai a tsakanin jama’a.
Bugu da kari, Sarkin ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da addu’o’i domin samun zaman lafiya da ci gaba a jihar Kano da kasa baki daya, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya wajen gina al’umma mai dorewa.
Haka zalika, ya yi addu’ar samun damina mai albarka domin tallafa wa harkokin noma da inganta rayuwar al’umma.
Sarkin ya kuma gargadi iyaye da masu kula da yara da su ba da muhimmanci ga tarbiyyar ‘ya’yansu, yana mai cewa kyakkyawar tarbiyya ita ce ginshikin gina al’umma mai nagarta.
Rahotanni sun nuna cewa manyan jami’an gwamnati da shugabanni sun halarci sallar, ciki har da jami’an gwamnatin jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki.

0 Comments:
Post a Comment