Iran ta shirya martani mai tsauri: “Abin da zai faru a yau ba kamar na jiya ba ne” — Ali Larijani
Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Koli ta Iran, Ali Larijani, ya bayyana cewa martanin sojin Iran da ake sa ran gani a yau zai kasance mai tsanani kuma daban da hare-haren da aka kai a jiya.
A wata sanarwa da ya fitar, Larijani ya ce kundin tsarin mulkin Iran ya tanadi hanyoyin da za a bi wajen tafiyar da al’amuran ƙasa idan aka samu gibi a shugabancin Jagoran Koli.
A cewarsa, an riga an kafa kwamitin shugabanci na rikon ƙwarya domin ci gaba da tafiyar da ayyukan Jagoran har zuwa lokacin da za a zaɓi magaji.
Ya yi bayani da cewa Mataki na 111 na Kundin Tsarin Mulkin Iran ya wajabta wa (Majalisar Kwararru) ta gaggauta zaɓen sabon Jagora idan aka samu rasuwa ko murabus ko tsige wanda ke kan mulki.
A lokacin jiran wannan nadin, Larijani ya ce wani kwamitin wucin gadi da ya ƙunshi Shugaban Ƙasa da Shugaban Ma’aikatar Shari’a da wani babban malamin addini daga Guardian Council ne ke da alhakin rike ayyukan Jagoran Koli.
Idan wani daga cikinsu bai iya ci gaba da aiki ba, doka ta tanadi a nemo wanda zai maye gurbinsa.
Dangane da tsaro, Larijani ya jaddada cewa rundunonin sojin Iran na tsaye daram wajen fuskantar duk wani yunƙuri da zai iya haddasa rikici ko rarrabuwar ƙasa, yana kira ga ‘yan ƙasa da su mara wa jami’an tsaro baya.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa a jiya Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka da na Israel, inda ya ce hare-haren sun yi tasiri sosai.
Sai dai ya yi gargaɗi da cewa abin da Iran ke shirin yi a yau zai fi na jiya ƙarfi da tsauri, yana mai nuni da cewa ƙasar ba za ta ja da baya ba wajen kare kanta.
News Translation in English Language.
Iran Warns of Harsher Response: “Today’s Action Will Be Different From Yesterday” — Ali Larijani
The Secretary of Iran’s Supreme National Security Council, Ali Larijani, has warned that Iran’s response today will be stronger and different from the strikes carried out the previous day.
Speaking in an official statement, Larijani said that Iran is acting in accordance with its constitution, which outlines clear procedures for managing state affairs in the event of a leadership vacuum. He confirmed that a temporary leadership committee has been formed to oversee the duties of the Supreme Leader until a successor is appointed.
Larijani cited Article 111 of Iran’s Constitution, which stipulates that if the Supreme Leader dies, resigns, or is removed, the Assembly of Experts must urgently convene to appoint a new leader.
Until that appointment is made, he explained, a provisional council comprising the President, the Head of the Judiciary, and a senior Islamic jurist from the Guardian Council will assume the responsibilities of the Supreme Leader. Should any member of this council be unable to continue, a replacement will be selected in line with constitutional provisions.
On the security situation, Larijani said Iran’s armed forces are working intensively to confront what he described as attempts to fragment the country, calling on the public to unite in support of the military.
He further confirmed that Iran launched missile strikes yesterday targeting military bases of the United States and Israel, stating that the attacks caused significant damage. He warned that Iran’s response today would be more severe, signaling a continued escalation.
Tags
Labarai
