Iran Ta Harba Makami Mai Cin Dogon Zango, yayin da IDF Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanarsa ga ƙasashen Turai.

Iran Ta Harba Makami Mai Cin Dogon Zango, yayin da IDF Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanarsa ga ƙasashen Turai.

Rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta sanar da cewa Iran ta harba wani makami mai linzami mai cin dogon zango a karon farko, wanda ake hasashen zai iya kaiwa nisan kusan kilomita 4,000.

A cewar IDF, wannan ci gaba na nuni da cewa irin wannan makami na iya kai hari zuwa wasu manyan biranen Turai, ciki har da Landan na Birtaniya da Paris na Faransa da kuma Berlin na Jamus.

Rahotanni sun bayyana cewa harba wannan makami na daga cikin matakan da ke kara tsananta rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke haddasa damuwa a tsakanin kasashen duniya kan yiwuwar fadada rikicin zuwa wajen yankin.

Sai dai wasu kasashe, ciki har da Birtaniya, sun jaddada cewa har yanzu babu cikakkiyar hujja da ke tabbatar da cewa akwai barazana kai tsaye ga Turai daga wannan makami.

News Translation in English Language.

IRAN TESTS LONG-RANGE MISSILE, IDF WARNS OF POTENTIAL THREAT TO EUROPE.

The Israeli Defense Forces (IDF) have announced that Iran has, for the first time, launched a long-range ballistic missile believed to have a range of approximately 4,000 kilometers.

According to the IDF, this development suggests that such a missile could potentially reach major European cities, including London in the United Kingdom, Paris in France, and Berlin in Germany.

Reports indicate that the missile launch is part of escalating tensions in the Middle East, raising concerns among the international community about the possible expansion of the conflict beyond the region.

However, some countries, including the United Kingdom, have stated that there is currently no conclusive evidence confirming an immediate or direct threat to Europe from the missile.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: