EFCC Ta Kwace Gidan Malami dake a Abuja.

EFCC Ta Kwace Gidan Malami dake a Abuja.

Jami’an Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun karɓe ikon mallakar gidan tsohon Ministan Shari’a na Tarayya (AGF), Abubakar Malami, da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun tare hanyar shiga gidan tare da hana zirga-zirga, kafin daga bisani su karɓe ikon sarrafa kadarar.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike da shari’o’i da suka shafi zargin almundahana da ake yi wa Malami, ciki har da batun kadarori da ake zargin ya mallake su ta hanyoyin da ba su dace ba. 

Tun da farko, wata kotu a Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace wasu kadarori da dama da ake dangantawa da tsohon ministan, wanda ya ƙara ƙarfafa matakan da hukumomi ke ɗauka a kansa. 

Rahotanni sun kuma nuna cewa wannan mataki na EFCC wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa tare da binciken dukiyoyin da ake zargin sun samo asali daga haramtattun hanyoyi.

News Translation in English Language.

EFCC Seizes Former AGF Malami’s Residence in Abuja.

Operatives of the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) have taken control of the residence of former Attorney-General of the Federation (AGF), Abubakar Malami, in Abuja.

Reports indicate that EFCC officials blocked access to the property and restricted movement before taking possession of the estate.

The action comes amid ongoing investigations and legal proceedings concerning allegations of corruption against Malami, including claims that he acquired certain assets through illicit means.

Earlier, a court in Abuja issued interim orders to seize several properties linked to the former minister, reinforcing the measures taken by the authorities.

Reports further indicate that the EFCC’s move is part of the government’s broader efforts to combat corruption and investigate assets suspected to have been acquired illegally.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: