Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka har yanzu ba ta shirya kulla wata yarjejeniya da Iran domin kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin bangarorin ba.
Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai, inda ya ce duk da cewa akwai alamun cewa Iran na son a samu tattaunawa, har yanzu Amurka ba ta ga sharuddan da za su dace da ita domin amincewa da wata yarjejeniya ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Amurka za ta ci gaba da matsin lamba kan Iran, yana mai jaddada cewa duk wata tattaunawa dole ne ta kasance bisa sharuddan da za su tabbatar da tsaron Amurka da kawayenta.
Trump ya kuma yi gargadin cewa Amurka na iya ɗaukar ƙarin matakan soja idan har rikicin ya ci gaba da ƙamari, musamman idan Iran ta ci gaba da barazana ga muradun Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa a duniya kan yiwuwar ƙara tsananta rikicin, wanda zai iya janyo matsaloli ga tsaro da tattalin arzikin duniya.
Rahoton ya nuna cewa har yanzu babu wata alama ta gaggauta cimma matsaya tsakanin bangarorin biyu kan batun tsagaita wuta ko yarjejeniyar zaman lafiya.
News Translation in English Language.
US Not Ready for Deal to End War With Iran — Donald Trump.
US President Donald Trump has said that the United States is not yet ready to enter into an agreement with Iran to end the ongoing conflict between the two sides.
Trump made the statement during an interview with a media outlet, noting that although there are indications that Iran is willing to engage in talks, Washington has not yet seen conditions that would make it acceptable to agree to a deal.
He added that the US government will continue to maintain pressure on Iran, stressing that any negotiations must be based on terms that guarantee the security of the United States and its allies.
Trump also warned that the United States could take additional military measures if the conflict escalates further, particularly if Iran continues actions that threaten US interests in the Middle East.
His remarks come at a time when global concerns are growing over the possibility of further escalation of the conflict, which could have serious implications for international security and the global economy.
Reports indicate that there are currently no clear signs that the two sides are close to reaching a ceasefire or peace agreement.

0 Comments:
Post a Comment