Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa a kusan shekaru 40 da ta yi da auren mijinta, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ba su taɓa ɗaga murya ga juna ba.
Ta bayyana hakan ne yayin wani taron buɗa-baki na haɗin gwiwa tsakanin Musulmi da Kiristoci (Iftar da Lent) da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda matan shugabanni da matan gwamnonin jihohi suka halarta.
Uwargidan shugaban ƙasar ta ce aurensu na addinai daban-daban ya kasance abin koyi na zaman lafiya da juna a Najeriya.
Ta ce:
> “Ni kusan shekaru 40 ina aure da Musulmi. Ba zan iya tuna lokacin da muka taɓa ɗaga murya ga juna ba—ko da sau biyu cikin waɗannan shekarun.”
Oluremi Tinubu ta kuma jaddada muhimmancin tsoron Allah wajen gina dangantaka mai ɗorewa, tana mai cewa duk wata alaƙa da mutum da ba shi da tsoron Allah ba ta daɗewa.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kawuna ta fuskar addini, tana mai cewa Musulmi da Kiristoci sun dade suna rayuwa tare cikin zaman lafiya.
Har ila yau, ta bukaci mata musamman waɗanda ke cikin muƙaman jagoranci ko matan shugabanni da su zama abin koyi wajen tarbiyyar matasa da kuma koyar da su kyawawan dabi’u.
News Translation in English Language.
First Lady on President Tinubu: “In 40 Years of Marriage, We Have Never Raised Our Voices at Each Other”
Nigeria’s First Lady, Oluremi Tinubu, has revealed that in nearly 40 years of marriage to President Bola Ahmed Tinubu, they have never raised their voices at each other.
She made the statement during a joint Muslim-Christian event marking Iftar and Lent at the Presidential Villa in Abuja, which was attended by spouses of governors and women leaders.
Oluremi Tinubu highlighted that their interfaith marriage serves as an example of peaceful coexistence in Nigeria. She said:
> “I cannot recall a single time we have raised our voices at each other in these almost 40 years of marriage.”
The First Lady also emphasized the importance of fearing God in building lasting relationships, noting that relationships without God’s guidance are unlikely to endure.
She urged Nigerians to avoid actions that could cause religious division, stressing that Muslims and Christians have long lived together in harmony. Oluremi Tinubu also called on women, particularly those in leadership roles, to set an example for young people and teach good values.
Tags
Labarai
