'Yan bindiga sun yi awan gaba da limamin babban masallacin Janjala dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.


Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da limamin babban masallacin Janjala, Malam Bello Abdullahi, shugaban Fulani a yankin, Alhaji Shehu Bello da wata mata a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

An ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun mamaye al’ummomi da dama da suka hada da Iddo, Gidan-Makeri, Kohoto, da Janjala, inda suka yi awon gaba da wasu mazauna garin tare da yin awon gaba da shanu. 

Bayan wadannan hare-haren da ba a saba gani ba, mazauna garin Kohoto, da ke makwabtaka da Janjala, sun bar gidajensu domin neman mafaka. 

Hakan ya biyo bayan wa’adin kwanaki bakwai da ‘yan bindigan suka yi wa al’ummar garin tare da taran Naira miliyan 6 domin sako matar da aka sace da ‘ya’ya hudu na wani dan banga a yankin.

Da yake tabbatar da sabon lamarin a ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026, wani shugaban al’umma ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a ranar Talata da misalin karfe 9 na dare.

Ya ce ‘yan bindigar sun yi awan gaba babban Limamin da shugaban Fulanin yankin da wata mata.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan bindigar da suka isa wurin da yawan gaske dauke da bindigogi kirar AK-47, sun fara kai farmaki gidan babban Limamin kafin su wuce gidan shugaban Fulanin. Wannan mamayar dai ya jefa al'ummar yankin cikin rudani, lamarin da ya tilastawa mazauna garin tserewa domin neman mafaka.

“Ko da nake magana da ku a yanzu, mutane da dama sun tsere daga gidajensu zuwa garin Kagarko, yayin da wasu kuma suna Sabon-Wuse suna zaune da ‘yan uwa,” inji shi.

Shugaban al’ummar ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare, inda ya ce ya aika da kiraye-kirayen nuna damuwa ga jami’an tsaro ba tare da samun amsa mai kyau ba.

“Mutanen mu na cikin kawanya, mun yi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro a Kagarko game da ‘yan bindigar da suka kai wa mutanen mu hari sama da mako guda, amma ba a yi komai ba,” in ji shi.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form