Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya isa kasar Oman domin tattauna batun Nukiliyan ƙasar da jami'an Gwamnatin Amurka

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya isa kasar Oman domin tattauna batun Nukiliyan ƙasar da jami'an Gwamnatin Amurka

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Abbas Araghchi ya isa kasar Oman domin tattauna batun Nukiliyan ƙasar da jami'an Gwamnatin Amurka bayan da aka shafe makonni ana takun saka da fargabar farkewar yaki a tsakanin kasashen biyu.

Iran za ta shiga tattaunawar ne "tare da Hukumomin Amurka da nufin cimma daidaito da karbuwa da fahimtar juna kan batun nukiliyar ƙasar," in ji kakakin ma'aikatar, Esmail Baghaei.

Baghaei ya kara da cewa, "Muna fatan bangaren Amurka zai kuma shiga cikin wannan tsari tare da daukar nauyi da gaskiya da kuma mahimmanci."

Surukin Shugaban ƙasar Amurka, Jared Kushner, da wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff ne zasu wakilci bangaren Amurka a tattaunawar.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form