‘Yan bindiga sun kashe mutane sama da 30 tare da ƙona gidaje da shaguna a jihar Kwara.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 35 tare da kona gidaje da shaguna a wani kauye mai suna Woro dake ƙaramar hukumar Kaiama a jihar Kwara, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Dan majalisar wakilai a yankin Kaiama, Sa’idu Baba Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kirga gawarwaki 35 zuwa 40
"Wasu da yawa sun tsere cikin daji da harbin bindiga," in ji Ahmed, ya kara da cewa za a iya samun karin gawarwakin.
Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai a wannan shekara a gundumar da ke kan iyaka da jihar Neja, wanda wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hare-haren.
Mazauna kauyukan sun tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye yayin da ‘yan bindigar suka kai hari kan Woro, kamar yadda Ahmed ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho. Ya ce har yanzu ba a ga mutane da dama ba.
‘Yan sanda sun tabbatar da harin, wadanda ba su bayar da adadin wadanda suka mutu ba. Gwamnatin jihar ta dora alhakin harin kan 'yan ta'adda".
Rikicin ‘yan fashin daji a yankunan karkara ya yi kamari a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a Najeriya a shekarun baya-bayan nan yayin da gungun ‘yan bindiga ke kai hare-hare a kauyuka, suna garkuwa da mutane tare da sace dabbobi.
Tags
Labarai
