An kashe dan sanda tare da wasu mutum 16 a wani hari da 'yan bindiga suka kai kasuwar kauye a jihar Benuwe.
Akalla mutane 17 ne suka mutu ciki har da dan sandan, bayan wani hari da wasu mahara dauke da makamai suka kai a wata kasuwar kauye da ke unguwar Abande da ke unguwar Mbaikyor a gundumar Turan a karamar hukumar Kwande a jihar Benue.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, harin wanda ya afku a ranar Talata, an kai shi ne a ranar kasuwar Abande, lokacin da mazauna yankin ke saye da sayar da kayayyaki.
Shi ma tsohon kansila mai sa ido a karamar hukumar Kwande, Akeregba Lawrence, ya ce maharan sun bude wuta kan ‘yan kasuwa da mazauna yankin, inda suka kashe mutane da dama nan take.
Ya ce sun kuma wawashe kayayyakin shagunan, inda ‘yan kasuwar suka yi zargin an kwashe tsabar kudi da kayayyaki sama da Naira miliyan 150 kafin su kona kasuwar baki daya.
Tags
Labarai
_3.jpeg)