Rahotanni daga kafafen yada labaran ƙasar Iran sun bayyana cewa, wani jirgin saman sojin kasar Iran ya fadi a tsakiyar wata kasuwar kayan marmari a karamar hukumar Dorcheh a lardin Isfahan a yau Talata.
Mutane hudu ne suka mutu a hadarin — matukin jirgin da mataimakinsa, da kuma mutane biyu daga cikin fararen hula da suke kasuwar a lokacin.
Jirgin ya fadi ne yayin da yake aiwatar da atisayen soji, Inda hadarin ya haifar da wuta wacce jami’an agaji suka kashe daga baya.
Masana sun ce yawaitan hadurran jiragen sama a Iran yana da Alaƙa da tsufan jiragen da ake amfani da su da kuma matsalolin samun kayan gyara sakamakon takunkumin kasashen Yamma.
Hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan wani jirgin yakin F‑4 ya fadi a lardin Hamadan, wanda ya kashe matukin jirgin ɗaya.
News Translation in English Language.
Iranian Military Helicopter Crashes into Fruit Market, Four Dead.
According to Reuters, an Iranian military helicopter crashed into a fruit market in Dorcheh, Isfahan province on Tuesday.
Four people were killed in the incident — the pilot and co-pilot of the helicopter, along with two civilians who were at the market at the time.
The helicopter was on a training flight when it went down, causing a fire that was extinguished by emergency responders.
Experts say Iran’s record of aviation accidents is poor due to aging aircraft and difficulty obtaining spare parts because of Western sanctions.
The crash comes less than a week after an F‑4 fighter jet crashed in Hamadan province, killing one pilot.
Tags
Labarai
