Trump Ya ba Iran Wa’adin Kwana 10 don cimma yarjejeniya da Amurka

Trump Ya ba Iran Wa’adin Kwana 10 don cimma yarjejeniya da Amurka

Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Iran na da wa’adin kwana 10 kacal don cimma wata muhimmiyar yarjejeniya da Amurka, in ba haka ba, za a iya ɗaukar wasu matakai na gaba.

Trump ya faɗi hakan ne yayin wani taron tattaunawa kan zaman lafiya, inda ya jaddada cewa Washington na son a warware rikicin shirin nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, amma ba zai yi ƙasa a gwiwa ba idan hakan ya gagara.

Rahoton ya nuna cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ta hanyoyi na ba kai tsaye, amma har yanzu akwai sabani kan muhimman batutuwa, musamman batun inganta sinadarin uranium da kuma shirye-shiryen makamai.

A daidai lokacin da ake tattaunawar, Amurka ta ƙara tura kayan soji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke nuna shirin ko ta kwana idan diflomasiyya ta gaza. Iran kuwa ta ce ba za ta janye haƙƙinta na ci gaba da shirin nukiliya ba.

Masana harkokin siyasa na ganin wa’adin kwanaki 10 da Trump ya bayar na iya zama muhimmin lokaci wanda zai yanke hukunci tsakanin cimma yarjejeniya ko ƙara tsananta rikici a yankin.

News Translation in English Language.

Trump Gives Iran 10-Day Deadline to Reach Deal with the United States

US President Donald Trump has said that Iran has 10 days to reach a meaningful agreement with the United States, warning that further steps could be taken if no deal is achieved.

Trump made the statement during a meeting focused on peace and diplomacy, stressing that Washington prefers a diplomatic solution to the standoff over Iran’s nuclear programme, but is prepared to act if talks fail.

According to the report, indirect negotiations between the two sides are ongoing, but major disagreements remain, particularly over Iran’s uranium enrichment activities and its broader military capabilities.

At the same time, the United States has increased its military presence in the Middle East, a move widely seen as a signal of readiness should diplomacy break down. Iran, however, has reiterated that it will not give up what it describes as its legitimate nuclear rights.

Political analysts say the 10-day deadline could prove to be a critical turning point, determining whether the crisis moves toward a diplomatic breakthrough or further escalation in the region.

Al Jazeera

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form