Tinubu ya bukaci a sako tsohon Fira ministan Sudan ta Kudu, Matare Machar don ci Gaban Zaman Lafiya a Ƙasar.

Tinubu ya bukaci a sako tsohon Fira ministan Sudan ta Kudu, Matare Machar don ci Gaban Zaman Lafiya a Ƙasar.

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga a sako ba tare da sharadi ba na Firam Ministan Farko na Sudan Ta Kudu, Riek Machar, da sauran shugabannin adawa da aka tsare, a matsayin mataki na tallafa wa zaman lafiya a kasar.

Kiran ya fito ne daga sanarwa da aka bayar yayin Taron Majalisar Manyan Shugabannin AU na Sudan Ta Kudu da aka gudanar a Addis Ababa na ƙasar Habasha, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilci Najeriya.

Najeriya ta sake tabbatar da goyon bayanta ga Sasantawar Zaman Lafiya da aka Sabunta, inda ta yi kira ga dukkan bangarori su shiga tattaunawa cikin lumana ba tare da sharaɗi ba, su yi aiki kan sulhu na kasa baki daya, da shirya zabe mai gaskiya.

Taron, wanda shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya jagoranta, ya nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wadda aka amince da ita shekaru takwas da suka wuce amma har yanzu tana cikin rauni.

Wasu shugabannin Afirka da kungiyoyi na yankin, ciki har da IGAD, sun jaddada bukatar sabunta sasanci da sanya ido don hana sake barkewar rikici a kasar.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form