Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa mutane sama da 100 a jihar Kwara.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a jihar Kwara wanda rahotanni suka ce an kashe mutane kusan 100.

A ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka kai wani kazamin hari a yankin Woro da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen, yayin da aka bayyana bacewar wasu mutane da dama.

A cikin wata sanarwa da kakakin babban sakataren MDD, Stéphane Dujarric ya fitar a ranar Alhamis, ya jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga Najeriya tare da goyon bayan kokarin gwamnatin kasar na yaki da ta'addanci.

Sanarwar ta ce, “Sakataren Janar na mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma jama’a da gwamnatin Najeriya, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

“Sakataren Janar na jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya tare da gwamnati da al’ummar Najeriya a kokarinsu na yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi tare da jaddada muhimmancin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form