Sabuwar Gobara ta sake tashi a Kasuwar Singer a jihar Kano

Sabuwar Gobara ta sake tashi a Kasuwar Singer a jihar Kano

Wata sabuwar gobara ta sake tashi a shahararriyar Kasuwar Singer, da ke kan titin Ado Bayero a cikin birnin Kano, inda ta lalata shaguna da dama tare da jawo asarar dukiyoyi masu yawa.

Rahotanni daga shaidu sun bayyana cewa an ga hayaki mai kauri da harshen wuta na tashi daga bangaren Gidan Gilas (Gidan Mai), lamarin da ya jefa ‘yan kasuwa da mazauna yankin cikin firgici yayin da suke kokarin ceto hajojinsu da hana gobarar bazuwa zuwa sauran sassan kasuwar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba. Jami’an kashe gobara da sauran hukumomin agaji sun isa wurin domin dakile yaduwar wutar da kuma rage barnar da take yi.

Wannan na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan wata gobara makamanciyar wannan ta afku a kasuwar, inda ta jawo asarar dukiyoyi na miliyoyin naira. Maimaituwar irin wadannan gobara na kara tada hankalin ‘yan kasuwa tare da haifar da tambayoyi kan matakan tsaro da inganta ababen more rayuwa a kasuwar.

Har yanzu ba a samu rahoton asarar rayuka ba, sai dai ana ci gaba da tantance girman barnar da gobarar ta haddasa.

Hukumomi sun ce za su gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar tare da daukar matakan da suka dace don kauce wa sake faruwar hakan a nan gaba.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form