Osimhen Ya Soki Salon Wasan Galatasaray Duk da Doke Juventus

Osimhen Ya Soki Salon Wasan Galatasaray Duk da Doke Juventus

Tauraron dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda Galatasaray ta buga wasa, duk da nasarar da ta kai su zagaye na gaba a Gasar Zakarun Turai bayan doke Juventus a jimillar kwallaye 7-5 a wasannin gida da waje .

Galatasaray ta samu nasarar yin waje da Juventus a karawar zagayen share fage zuwa matakin 'yan 16 na gasar ta UEFA Champions League, bayan fafatawa mai cike da rudani da tashin hankali wanda aka tashi wasan 3-2 a gidan Juventus, lamarin da ya ba Galatasaray nasara da jimillar kwallaye 7-5 akan Juventus din. 
Sai dai Osimhen, wanda ya taka rawar gani a wasan, ya bayyana cewa sakamakon bai kamata ya rufe gazawar da aka gani a filin wasa ba.

A cewarsa, ‘yan wasan Galatasaray da dama sun nuna fargaba da rashin kwarin gwiwa, lamarin da ya bai wa Juventus damar dawowa cikin wasa. Ya ce dole ne kungiyar ta gyara kura-kurenta idan tana son yin nisa a gasar, musamman ganin irin manyan kungiyoyin da ke jira a zagaye na gaba.

Osimhen ya kara da cewa nasara a irin wannan mataki na gasar ba ta isa a yi murna da ita ba idan aka buga wasa ba tare da tsari da kwazo ba. Ya jaddada bukatar kara dagewa, hadin kai da jajircewa domin fuskantar manyan kalubale masu zuwa.

Duk da wadannan kalamai masu zafi, Galatasaray ta ci gaba da tafiya zuwa zagaye na gaba, inda ake sa ran za ta fuskanci babbar jarabawa a neman daukaka a gasar ta zakarun nahiyar Turai.

News Translation in English Language.

Osimhen Criticises Galatasaray’s Performance Despite Victory Over Juventus.

Nigerian striker Victor Osimhen has expressed dissatisfaction with Galatasaray’s overall display, despite the club’s qualification after defeating Juventus in the UEFA Champions League.

Galatasaray progressed in the UEFA Champions League following a tense and dramatic two-legged encounter against the Italian giants. However, Osimhen, who played a decisive role in the tie, insisted that the result masked several shortcomings in his team’s performance.

Speaking after the match, the Nigerian forward said a number of Galatasaray players appeared nervous and lacked composure, allowing Juventus to gain momentum at critical stages of the contest. He stressed that such lapses could prove costly against stronger opponents in the next round.

Osimhen noted that advancing in the Champions League should not be an excuse to overlook poor execution and tactical errors. According to him, the team must show greater confidence, discipline and collective responsibility if it hopes to compete at the highest level in Europe.

Despite the criticism, Galatasaray have secured their place in the next stage of the competition, where tougher challenges are expected as the race for continental glory intensifies.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form