Hukumar DSS Ta Saki Walida, ya yin da aka mika ta ga Gwamnan Jigawa

Hukumar DSS Ta Saki Walida, ya yin da aka mika ta ga Gwamnan Jigawa

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS, ta saki Walida Abdulhadi Ibrahim bayan makonni tana tsare da ita, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar.

Bayan sakin nata, DSS ta mika Walida ga Umar Namadi, Gwamnan Jihar Jigawa, domin ci gaba da bin doka da tabbatar da kare hakkokinta.

Tun da farko, iyalan Walida sun zargi wani jami’in DSS da sace ta tare da tilasta mata sauya addini, inda suka ce tana karama a lokacin da lamarin ya faru. 
Sai dai DSS ta ce tana rike da ita ne domin kariya, saboda ta bayyana tsoron komawa gida.

Kungiyar kare hakkin Musulmi, Muslim Rights Concern (MURIC), da sauran kungiyoyi sun yi ta matsin lamba, suna bukatar a bi umarnin kotu na sakin Walida tare da mayar da ita ga iyayenta.

Rikicin ya kara daukar hankali ne sakamakon sabanin ra’ayi kan shekarun Walida da kuma ko ta tafi da son ranta ko akasin haka. Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta tabbatar da adalci da bin doka yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Masu sharhi na ganin sakin Walida na iya kawo sabon salo a shari’ar, tare da fatan za a warware rikicin cikin adalci da zaman lafiya.

News Translation in English Language.

DSS Releases Walida, Hands Her Over to Jigawa Governor.

Nigeria’s secret police, the Department of State Services (DSS), has released Walida Abdulhadi Ibrahim after weeks in custody, a case that sparked widespread public and legal controversy.

Following her release, Walida was handed over to Umar Namadi, the Governor of Jigawa State, for further handling in line with due process and the protection of her rights.

Earlier, Walida’s family accused a DSS operative of abducting her and forcing her to convert her religion, insisting that she was a minor at the time of the alleged incident. The DSS, however, maintained that she was kept in protective custody, claiming she expressed fear of returning to her family.

The Muslim Rights Concern (MURIC) and other Muslim organisations had mounted pressure on the DSS to obey a court order directing Walida’s immediate release and reunification with her parents.

The matter drew national attention due to conflicting accounts over Walida’s age and whether she left home voluntarily or was abducted. The Jigawa State Government has assured the public that it will ensure justice, transparency, and adherence to the rule of law as investigations continue.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form