Ofishin Jakadancin Indiya a Iran ya gargadi dukkan ‘yan ƙasar Indiya da ke Iran, ciki har da dalibai da masu aikin addini da ‘yan kasuwa, da masu yawon shakatawa, da su bar kasar nan take ta kowanne irin hanyar sufuri da ake da shi, ciki har da jiragen kasuwanci.
Sanarwar ta jaddada cewa yanayin tsaro na iya ƙara taɓarɓarewa cikin gaggawa, musamman a yayin da ake fargabar tsanantar rikici tsakanin Iran da Amurka.
Saboda haka, an shawarci ’yan Indiya da su guji taruka, zanga-zanga da wuraren da ke da hatsari, tare da kasancewa a hulɗa kai tsaye da jakadancin ƙasarsu.
Hakanan, ‘yan Indiya a Iran an shawarce su da su tanadi takardun tafiya da shaidar su a kowane lokaci, sannan su yi rijista da ofishin jakadancin ta yanar gizo.
An kuma bukaci iyalai a Indiya su taimaka wajen yin rijista idan aka samu katsewar intanet a Iran.
Gargadin ya sake jaddada shawarwari da aka bayar a ranar 5 da 14 ga Janairu, inda aka bayyana cewa tsaron ‘yan kasa shi ne babban abin da ake fifitawa.
News Translation in English Language.
India Urges Citizens to Leave Iran as Security Tensions Escalate.
Tehran — The Government of India has issued a fresh advisory urging its citizens currently in Iran to leave the country immediately using all available means, citing a rapidly deteriorating security situation.
In a statement released by the Embassy of India in Tehran, Indian nationals—including students, businesspeople, pilgrims, and tourists—were advised to exercise extreme caution and avoid public gatherings, protests, and areas prone to unrest.
The advisory warned that the situation could worsen without notice amid heightened regional tensions, raising concerns for the safety of foreign nationals. Citizens have been asked to remain in close contact with the Indian mission, keep their travel and identity documents readily accessible, and register their details with the embassy to facilitate assistance if required.
This latest warning follows similar advisories issued earlier, as New Delhi steps up efforts to ensure the safety and well-being of its nationals abroad in an increasingly volatile regional environment.
Tags
Labarai
