Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Lissafa Najeriya a cikin jerin kasashe Biyar da suka fi kowa yawan Ɗaukar Yara aikin Soji.

Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Lissafa Najeriya a cikin jerin kasashe Biyar da suka fi kowa yawan Ɗaukar Yara aikin Soji.

Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta bayyana cewa Najeriya na cikin kasashe biyar da ke da alkaluman yawan ɗaukar yara cikin aiki soji, a rahoton da aka fitar gabannin Ranar Duniya ta Yaki da Amfani da Yara aikin Soji.

Vanessa Frazier, Waliyar Musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yara da Rikicin Soja, ta ce ɗaukar yara da amfani da su a matsayin sojoji ko masu aiki a rundunonin tsaro da ƙungiyoyin ‘yan bindiga yana ci gaba da zama babbar matsala a duniya. 
A shekarar 2024 kadai, an tabbatar da cewa fiye da yara 7,400 ne aka ɗauke su ko kuma aka yi amfani da su a rikice-rikice a fadin duniya.

Rahoton ya nuna cewa mafi yawan wannan zalunci an same shi ne a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da Najeriya da Somalia da Siriya da Myanmar, wanda ke nuna irin hatsarin da yara ke fuskanta a yankunan da rikici ya shafa.

Frazier ta jaddada cewa duk kididdigar nan tana bayanin rayuwar yara da aka lalata saboda yaki, inda ta ce shirin UN ya taimaka wajen raba yara sama da 220,000 daga ƙungiyoyin sojoji cikin shekaru talatin da suka gabata, amma ta yi gargadi cewa sake haɗa su cikin al’umma na ci gaba da wahala saboda da tsananin damuwa da kunci da yawancin yaran suka fuskanta, musamman mata.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga ƙasashe da ƙungiyoyi su ƙara ƙoƙari wajen hana ɗaukar yara da kare su da tabbatar da hukunci ga masu aikata waɗannan laifuka, tana mai cewa ba za a samu zaman lafiya mai ɗorewa ba idan hakkin yara da makomarsu aka yi watsi da su.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form