Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa Addis Ababa babban birnin Habasha, domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a Taron Majalisar Shugabannin Kasashen Afirka Karo na 39.
Taron zai gudana ne daga ranar 14 zuwa 15 ga Fabrairu, 2026.
A tashar jirgin sama ta Bole International Airport, Shettima ya samu tarbar manyan jami’an Habasha, ciki har da Dr. Belete Mola, Ministan Kirkire-Kirkire da Fasaha, da Amb. Berhanu Tsegaye, Ministan Harkokin Waje na Jihar. Haka kuma, manyan jami’an diflomasiyya na Najeriya da suka hada da Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar da sauran wakilan gwamnatin tarayya sun kasance a wurin tarbar sa.
Mataimakin Shugaban Kasa zai wakilci Shugaba Tinubu wajen tattaunawa kan manyan manufofin ci gaban Afirka da hadin gwiwa tsakanin kasashen nahiyar.
A gefe guda, an shirya cewa zai yi ganawa ta musamman da shugabannin siyasa da kasuwanci domin karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Taron AU na 39 zai mayar da hankali kan ci gaban nahiyar, hadin kan kasashen Afirka, da sauran muhimman al’amura da suka shafi dorewar tattalin arziki da cigaban al’umma.
Tags
Labarai
