Babban kifin da aka kama a bana a bikin raya al'adu da kamun kifi na Argungu ya kai nauyin kilo 59, lamarin da ya zama abin alfahari da jan hankali a gasar kamun kifi ta bana da aka gudanar a Argungu, Jihar Kebbi.
Bikin na bana, wanda shine karo na 61, ya fara ne a ranar Juma’a, 14 ga Fabrairu, 2026, a filin Matan Fada.
Dubban masunta daga sassa daban-daban na jihar da ma ƙasar nan sun hallara domin fafatawa a gasar da ta kasance ginshiƙin bikin.
Rahotanni sun nuna cewa sama da masunta 40,000 ne suka taru bakin kogi tun da sassafe kafin fara gasar a hukumance, yayin da dubban jama’a suka yi cincirindo domin kallo da murnar bikin.
Bikin Kamun Kifi na Argungu na ɗaya daga cikin manyan bukukuwan gargajiya a Najeriya, wanda aka assasa tun a shekarar 1934 domin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasa yawon buɗe ido.
Baya ga gasar kamun kifi, bikin na Æ™unshe da nune-nunen al’adu da suka haÉ—a da raye-raye da wake-wake da kokawa da sana’o’in gargajiya da sauran wasanni, lamarin da ke Æ™ara jawo hankalin baÆ™i daga sassa daban-daban na cikin gida da Æ™asashen waje.
Tags
Labarai
