Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da “Kisan” Mutanen Falasdinu a lokacin taron ta karo na 39 a Addis Ababa.

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da “Kisan” Mutanen Falasdinu a lokacin taron ta karo na 39 a Addis Ababa.

A yayin taron kolin shugabannin Tarayyar Afirka (AU) na 39, shugabannin kasashen Afirka sun yi kira da a kawo karshen abin da suka kira “kisan” al’ummar Falasdinu, dangane da rikicin da ke gudana a Gaza.

Shugabannin sun jaddada cewa dole ne a kiyaye dokokin kasa da kasa da na jin kai, tare da yin kira da a sauke takunkumin da ke hana shigar kayan agaji Zirin Gaza.

Bugu da kari, shugaban AU ya yi tsokaci kan yadda rikice-rikice a kasashen Afirka, ciki har da Sudan da Sahel da Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo (DRC) da Somaliya, ke ci gaba da jefa al’ummar Afirka cikin matsananciyar wahala, inda ya sake yin kira da a “daina yin anfani da makamai” a nahiyar.

Taron ya kuma mayar da hankali kan canjin yanayi da kalubalen shugabanci da batutuwan ruwa da tsaftar muhalli a kasashen Afirka.

A yayin taron, Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yaba da rawar AU wajen tattaunawa da hadin kai a duniya, sannan ya sake jaddada bukatar Afirka ta samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaro ta MDD.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form