Hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa biyu a zirin Gaza a lokacin watan Ramadan.

Hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa biyu a zirin Gaza a lokacin watan Ramadan.

Hare-haren sojojin Isra’ila a Zirin Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutane biyu Falasdinawa, tare da jikkata wasu da dama, duk da da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Rahotanni daga asibitoci sun ce hare-haren sun faru ne a wasu yankuna kamar Jabalia da kusa da Khan Younis, inda aka yi amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa da sauran makamai. 
Wannan ya faru ne a farkon kwanakin azumin watan Ramadan, abin da ya ƙara tayar da hankula a yankin.

Hukumomi a Gaza sun bayyana cewa wannan hari na daga cikin karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a baya, inda har yanzu ake samun hare-hare da luguden wuta a sassa daban-daban na yankin.

A halin da ake ciki, al’ummar Gaza na ci gaba da fuskantar matsanancin yanayin jin ƙai, saboda yawan ‘yan gudun hijira da ƙarancin abinci da magunguna, duk da buɗe wasu hanyoyin shigar da kayan agaji da fitar da marasa lafiya.

Rikicin Isra’ila da Falasɗinu na ci gaba da ɗaukar hankali a duniya, yayin da ake fargabar ƙarin tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form