Fashewar Bam da ake Zargin IED ne ta Girgiza Sakatariyar Gwamnatin Bayelsa a Yenagoa
An tayar da bam da ake zargin na’urar fashewar hannu ce ta (Improvised Explosive Device – IED) a safiyar yau Laraba a Cibiyar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Bayelsa da ke Yenagoa.
Fashewar ta haddasa daukar matakan gaggawa daga jami’an tsaro tare da dakatar da ayyukan gwamnati na dan lokaci.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safe, inda Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bayelsa ta dauki mataki cikin gaggawa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bayelsa, CP Iyamah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, inda ya ce ba a samu asarar rai ko barnatar dukiya ba.
A cewarsa, “A halin yanzu ana yi wa wanda ake zargi tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID), kuma bayan kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Ina sanar da jama’a cewa al’amura suna karkashin kulawa kuma an dawo da zaman lafiya. Muna shawartar al’umma da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da harkokinsu yadda ya kamata.”
Biyo bayan faruwar lamarin, Gwamnatin Jihar Bayelsa ta bayar da umarnin rufe ofisoshin gwamnati na tsawon sa’o’i hudu, a matsayin matakin kariya. Wannan mataki ya shafi sama da ma’aikatan jiha 6,000.
Umarnin ya fito ne daga Shugaban Ma’aikatan Jihar, Dr Wisdom Ebiye Sawyer.
Jami’an tsaro, ciki har da rukunin yaki da bama-bamai, sun killace hanyoyin da ke kaiwa Sakatariyar Jihar Bayelsa da Fadar Gwamnatin Jihar, yayin da ake ci gaba da bincike da aiwatar da ka’idojin tsaro.
Hukumomi sun bayyana cewa an shawo kan lamarin gaba daya.
Tags
Labarai
