ƙasar Oman Ta Fitar da Ranar Fara Azumi Bisa Lissafin Ilimin Taurari.

ƙasar Oman Ta Fitar da Ranar Fara Azumi Bisa Lissafin Ilimin Taurari.

Ƙasar Oman ta sanar da cewa ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu, 2026, ita ce ranar farko ta watan Ramadan na shekarar Hijira 1447AH, bisa lissafin ilimin taurari wanda ake kira (astronomical calculations) a turance.

Rahotanni sun nuna cewa kwamitin duba jinjirin wata a Oman ya bayyana cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Ramadan ba a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wadda ita ce ranar 29 ga watan Sha’aban. Hakan ya biyo bayan bayanan masana ilimin taurari da suka nuna cewa watan zai fadi kafin faduwar rana ko kuma daidai lokacin faduwar rana, lamarin da ke hana yiwuwar ganinsa da ido a fadin kasar.

Saboda haka, Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026 za ta kasance rana ta cikar watan Sha’aban, yayin da Alhamis, 19 ga Fabrairu, za ta zama ranar farko ta azumin Ramadan a ƙasar Oman.

Masu sharhi kan harkokin addini sun bayyana cewa wannan matsaya ta Oman ta dace da bayanan kimiyya da na ilimin taurari, kuma ta yi daidai da hasashen wasu cibiyoyin binciken taurari a yankin Gulf, wadanda su ma suka nuna cewa ba za a iya ganin jinjirin watan Ramadan ba a ranar 17 ga Fabrairu.

Sai dai, kamar yadda aka saba a kasashen Musulmi da dama, hukumar duba wata ta kowace kasa ce za ta tabbatar da ranar fara azumi bisa tsarin da take bi, ko dai ta hanyar gani da ido ko kuma ta amfani da lissafin ilimin taurari.

Rahoton ya nuna cewa Ramadan 2026 na iya fara ne a rana guda a yawancin kasashen yankin Gulf, idan aka bi wannan hasashe na kimiyya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form