Jihohin Minas da Gerais na ƙasar Brazil sun fuskanci mummunar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama a wannan watan.
Biranen Juiz de Fora da Ubá sune mafi muni inda gidaje da hanyoyi suka lalace.
Aƙalla mutane 46 ne suka rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman mutane 21 da ake zargin sun bace.
Fiye da mutane 3,000 sun rasa matsugunansu, inda jami’an ceto da masu aikin sa‑kai ke cigaba da kokarin ceto wadanda wannan ambaliya ta shafa.
Rahotanni sun nuna cewa yawan ruwan sama a watan Fabrairu ya ninka da kashi biyu na yadda ake tsammani, lamarin da ya ƙara tsananta ambaliyar da gushewar ƙasa a wasu wurare.
Daga cikin wadanda suka mutu, akwai yaro mai shekara 11, abin da ya jefa al’umma cikin ƙunci.
Hukumomi na ci gaba da bada tallafi ga waɗanda suka tsira, tare da ƙoƙarin dawo da mutanen da suka bace.
Masana na gargadin cewa irin wannan ruwan sama mai yawa na iya janyo karin ambaliyar ruwa a nan gaba idan ba a ɗauki matakan kariya ba.
News Translation in English Language.
Brazil Floods Leave 46 Dead, Thousands Displaced in Minas Gerais.
Minas Gerais, Brazil — Severe rainfall in southeastern Brazil has triggered devastating floods and landslides, particularly affecting the cities of Juiz de Fora and Ubá, destroying homes and infrastructure.
Authorities have confirmed that at least 46 people have died, while 21 others remain missing. More than 3,000 residents have been displaced, prompting emergency crews and volunteers to continue rescue and relief operations.
Meteorologists reported that February rainfall was more than double the usual average, worsening the floods and triggering landslides. Among the victims was an 11-year-old child, highlighting the human toll of the disaster.
Officials continue to provide aid to survivors and search for the missing, warning that such extreme flooding could recur if preventive measures are not implemented.
Tags
Labarai
