Harin dai ya afkawa yaran ne a kusa da asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza a lokacin da suke tattara itacen girki, kamar yadda majiyoyi suka bayyana.
Falasdinawa da ke zaune a cikin tantuna na wucin gadi ba su da wani kariya daga iska mai ƙarfi da matsanancin sanyi da ruwan sama, saboda yawancin matsugunan an yi su ne da siraran abun rufi na robobi, Wanda hakan ke tilastawa Falasdinawan neman makamashin da zasu kona domin dumama inda suke kwana baya ga wanda zasu yi girki.
Sai dai duk da wannan mawuyacin hakin da Al'ummar Gaza ke ciki har yanzu Isra'ila na ci gaba da hanawa ko takaita adadin muhimman kayan agaji da ke shiga cikin yankin, kamar tantuna da katifun kwanciya da barguna, wanda hakan ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta cimma da Kungiyar Hamas a watan Oktoban 2025, da kuma wajibci a karkashin dokokin kasa da kasa.
