Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ‘Yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar yunwa a shekarar 2026.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ‘Yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar yunwa a shekarar 2026.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ‘Yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar yunwa a shekarar 2026.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, ta ofishinta dake kula da ayyukan jin kai a Najeriya cewa, kimanin ‘yan Najeriya miliyan 35 ne ke fuskantar barazanar yunwa a bana, ciki har da yara miliyan 3 da ke fuskantar matsananciyar rashin abinci mai gina jiki. 

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairu, biyo bayan rugujewar kasafin kudin agaji na duniya. 

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin jin kai na shekarar 2026 a Abuja, babban jami’in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Mohamed Malick Fall, ya ce tsarin bayar da agajin da aka dade a Najeriya, da kasashen waje ke jagoranta ba zai dore ba, kuma bukatun Najeriya sun karu. 

Halin da ake ciki a yankin arewa maso gabas da ke fama da tashe-tashen hankula, inji Fall, inda fararen hula a jihohin Borno, Adamawa da Yobe ke fuskantar tashin hankali, yawaitar hare-haren bama-bamai da kuma hare-haren wuce gona da iri sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 4,000 a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, wanda ya yi daidai da adadin da aka samu a shekarar 2023, in ji shi.

Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta samar dala miliyan 516 ne kawai domin agajin ceto ga mutane miliyan 2.5 a bana, wanda ya ragu daga miliyan 3.6 da ta samar a shekarar 2025, wanda hakan ya kai rabin adadin shekarar da ta gabata. 

"Waɗannan ba ƙididdiga ba ne kawai, lambobi ne dake wakiltar rayuwa da makomar 'yan Najeriya," in ji Fall. 

Ya kuma ce Majalisar Dinkin Duniya ba ta da wani zabi illa ta mai da hankali kan ayyukan "mafi ceton rai" sakamakon raguwar kudaden da ake samu. 

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form