Gwamnatin Sokoto ta gudanar da addu'o'in zaman lafiya da hadin kai.

Gwamnatin Sokoto ta gudanar da addu'o'in zaman lafiya da hadin kai.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin jihar Sakkwato ta gudanar da wani taron addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da hadin kai da ci gaban Nijeriya a Sakamakon matsalolin tsaro da tattalin arzikin kasa.

Addu'ar wacce aka gudanar a Masallacin Juma’a na Sultan Bello jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a, ta samu halartar manyan malaman addini da manyan jami’an gwamnati.

Da yake gabatar da addu'o'in, Sarkin Malaman Sokoto, Sheikh Yahaya Na Malam Boyi, ya roki Allah ya shiryar da shugabannin Najeriya yayin da suke tafiyar da harkokin kasa.

Daga karshe ya yi addu’a ga Gwamna Ahmad Sokoto, inda ya roki Allah ya kara masa kwarin guiwar kawo sauyi a jihar.

Gwamna Aliyu, Mataimakin Gwamna Idris Mohammed Gobir, tsohon Mataimakin Gwamna Mukhtar Shagari, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jiha Tukur Bala Bodinga, Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid, da manyan masu rike da sarautar gargajiya, ‘yan majalisa, kwamishinoni, shugabannin siyasa, da sauran manyan baki ne suka halarci taron.

Jami’an gwamnati sun ce taron addu’o’in wani bangare ne na kokarin samar da zaman lafiya da kuma nuna goyon baya ga zamantakewa da karuwar tattalin arzikin Najeriya.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: