Kungiyar kwallon kafa ta Super eagles zata fafata da Kasar Masar domin neman mataki na uku na cin kofin nahiyar Afrika AFCON da misalin karfe 5pm.
Kungiyar ta yi rashin nasara ne a hannun mai masaukin baki, Morocco a ranar laraba da ci 4-2 a bugun fanareti bayan da aka tashi wasan 0-0.
Ita kuwa Kasar Masar tayi rashin nasara ne a hannun Senegal da ci 1-0 mai ban haushi a wasan da suka buga ranar laraba.
A gobe lahadi za'a buga wasan karshe tsananin mai masaukin baki Morocco da Senegal domin fitar da zakaran gasar na wannan shekaran.

0 Comments:
Post a Comment