Aƙalla mutane 7 ne suka mutu, yayin da 82 suka bace bayan zaftarewar kasa a yankin Bandung na ƙasar Indonesiya.
Iftala'in na baya-bayan nan ya zo ne 'yan makonni bayan mummunar ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa ta kashe mutane fiye da 1,000 a yammacin ƙasar.
Abdul Muhari, mai magana da yawun hukumar kula da iftala'i na ƙasar, ya ce "adadin wadanda suka bace ya yi yawa, don haka za mu yi kokarin inganta ayyukanmu na ceto a yau."
Kamfanin dillancin labarai na Indonesiya Kompas, ya ce zaftarewar kasar ta afku ne a kauyen Pasirlangu da ke yammacin Bandung da misalin karfe 2 na safe agogon kasar a safiyar Asabar (19:00 agogon GMT a ranar Juma'a).
Kompas ya ba da rahoton cewa “kwararwar ruwa mai ƙarfi” da ƙasa maras kyau daga gangaren Dutsen Burangrang sun farfasa gidaje kusan 30 yayin da yawancin mazaunansu ke barci.
"Har yanzu ana ci gaba da lissafa adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata," in ji Kompas, yana mai ba da rahoton cewa ruwan sama mai karfi ya mamaye yankin a 'yan kwanakin nan.
Saboda fargabar sake afkuwar bala'in, hukumomin yankin sun ba da umarnin kwashe mazauna yankunan da aka san cewa ana iya samun zabtarewar kasa.
An kiyasta yankin da zaftarewar kasa ta shafa ya kai hekta 30, in ji Kompas.
Haka zalika Hukumar kula da yanayi ta Indonesiya ta yi gargadi game da matsanancin yanayi, ciki har da ruwan sama kamar da bakin kwarya a lardin yammacin Java na mako guda daga ranar Juma'a, a cewar rahotanni.
