Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce akwai yiwuwar Isra'ila ta kai hari akan Iran idan ta samu dama.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce akwai alamun Isra'ila na neman wata dama ta kai wa Iran hari, yana mai gargadin irin wannan matakin na iya kara dagula zaman lafiyar yankin.
"Ina fatan za su sami wata hanya ta daban, amma gaskiyar magana ita ce Isra'ila musamman na neman wata dama ta kai wa Iran hari," Fidan ya shaidawa gidan talabijin na NTV na Turkiyya a wata hira da aka watsa a ranar Juma'a.
Ministan harkokin wajen kasar ya kara da cewa ya mika damuwarsa kai tsaye ga jami'an kasar Iran a ziyarar da ya kai kasar.
"Lokacin da na je Tehran a cikin 'yan kwanakin nan, na gaya musu komai game da tsarin a matsayinsu na abokan mu," in ji Fidan. "Kuma ka sani, aboki yana faÉ—in gaskiya mai É—aci," in ji shi.
Tags
Labarai
