Takaitaccen Tarihin Marigayi Yahaya Sinwar, tsohon Jagoran Hamas a Gaza.

Takaitaccen Tarihin Marigayi Yahaya Sinwar, tsohon Jagoran Hamas a Gaza.

An haifi Sinwar a ranar 19 ga Oktoba, 1962, a sansanin 'yan gudun hijira na Khan Younis a kudancin Gaza, kuma iyalinsa sun gudu daga Majdal, wani birni da Isra’ila ta mamaye a shekarar 1948. Ya yi karatu a Makarantar Sakandare ta Khan Younis kuma daga baya ya kammala digirinsa a fannin nazarin harshen Larabci daga Jami'ar Islama ta Gaza.

‎Sinwar ya fara shiga harkokin siyasa lokacin yana jami’a a matsayin memba na Kungiyar Islama, reshen dalibai na 'Yan Uwan Musulmi a Falasdinu. Ya rike mukamai daban-daban na jagoranci a majalisar dalibai na Jami'ar Islama kuma ya taimaka wajen kafa wata kungiyar tsaro da ake kira "Mujahid," mai alhakin gano da bin diddigin masu hada kai da 'Isra’ila'.

‎An chafe Sinwar ne a shekarar 1982 saboda harkokin dalibanci. A tsawon shekaru, an tsare shi sau da dama, an yanke masa hukuncin rai da rai sau hudu tare da karin shekaru 426 saboda hadin kai a cikin garkuwa da kashe sojojin Isra’ila da kuma kisan Falasdinawa guda hudu da ake zargin suna hada kai da mamayar Isra’ila. A lokacin da yake tsare, ya jagoranci kungiyar jagorancin fursunonin Hamas kuma ya shirya yajin cin abinci da dama kan hukumomin gidan yari.

‎A shekarar 2011, an sako Sinwar a cikin musayar fursunoni da sojan Isra’ila Gilad Shalit, bayan shafe fiye da shekaru biyar a tsare. 

‎Bayan an sake shi, cikin hanzari ya zama jigo a cikin Hamas, inda ya karbi nauyin shugabantar reshen soji, Al-Qassam Brigades.

‎An zabe shi shugaban Hamas a Gaza a shekarar 2017 kuma aka sake zabar shi a shekarar 2021, Sinwar ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun soja da siyasa a cikin kungiyar. Ya taka rawa a manyan ayyukan soja, ciki har da Yakin Gaza na 2014, inda ya duba ayyukan shugabannin filin daga kuma ya aiwatar da canje-canje a shugabanci da suka dace.

‎Sinwar an nada shi shugaban tattaunawar game da fursunonin Isra’ila da Hamas ke rike da su, kuma ya zama babban makasudin kisan gilla daga Isra’ila saboda rawar da yake takawa a kungiyar. Hauhawar rikice-rikicen baya-bayan nan ya kara daukaka rawar da yake takawa a cikin rikicin da ke gudana a yanzu.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: