Labarin wasanni: Najeriya ta doke Lesotho da ci 2-1

Labarin wasanni: Najeriya ta doke Lesotho da ci 2-1

Kungiyar kwallon kafar Super eagles ta Najeriya ta samu nasaran doke Kungiyar kwallon kafar kasar Lesotho da ci 2-1 a wasan share fagen shiga gasar cin kofin Duniya na 2026 da za'a buga a kasar Amurka da Canada da Mexico.

Sai dai duk da wannan nasaran da Najeriya ta samu akan kasar Lesotho zuwanta gasar na 2026 na kila wa kala ne saboda nasaran da kasar Jumhuriyar Benin ta samu akan Rwanda da ci 1-0 Wanda hakan ya ba Jumhuriyar Benin damar jagorantar rukunin da maki 17 sai Afrika ta kudu wacce keda maki 15 sai Najeriya Mai maki 14.

Hakan na nuna cewa Najeriya zata samu gurbi a gasar ta badi ne kawai idan ta samu nasara akan kasar Jumhuriyar Benin da ci 2-0 ko fiye da haka a wasan da zasu buga ranar Talata a birnin Uyo sannan Kuma idan kasar Rwanda da Afrika ta kudu suka yi chanjaras ko Kuma aka doke Afrika ta kudun.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: