Kasashe hudu (4) da zasu fafata domin fitar da wacce zata wakilci nahiyar Afrika a wasannin kifa daya kwala na cin kofin Duniya na 2026, inter-confederation play-offs a kasar Mexico.
Nigeria da Gabon zasu kece raini a wasan kifa daya kwala don fitar da kasar da zata wakilci nahiyar Afrika a inter-confederation play-offs .
Nigeria da Gabon zasu kece raini a wasan kifa daya kwala don neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya na 2026.
Kasashen Najeriya da Gabon da
Kamaru da Jumhuriyar Dimokwaradiyar Congo sune Kasashe hudun da zasu fafata a tsakaninsu domin fitar da Wanda zai wakilci nahiyar Afrika a inter-confederation play-offs da za'a fafata a kasar Mexico a watan Maris na 2026.
Najeriya zata kece raini da Gabon a Ranar 13 ga watan nuwanban Yayin da Kamaru zata fafata da Jumhuriyar Dimokwaradiyar Congo a Ranar 14 ga watan nuwanban.
A Ranar 16 ga watan nuwanba Kasashen da suka yi nasara zasu kece raini a wasan karshe domin fitar da kasar da zata wakilci nahiyar Afrika a wasannin inter-confederation play-offs.
Za'a samu wakilcin kasa daya daga nahiyoyin AFC, CAF, CONMEBOL da OFC Yayin da Kasashe biyu zasu wakilci nahiyar CONCACAF domin fafatawa wajen cike gurbin Kasashe biyu a gasar cin kofin Duniya na 2026.

0 Comments:
Post a Comment