Afolabi Olumide Ayodeji ya zama dalibin da yafi kowane dalibi samun maki mai yawa jarabawar share fare shiga Jami'a JAMB ta bana 2025 Inda ya samu jimullan maki 370.
Dalibin ya samu maki a darusa kamar haka:
Mathematics – 98
Physics – 98
Chemistry – 94
English. – 80.
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta tabbatar da cewa babu wani mutum da ya samu maki 370 tun a kalla a shekarar 2013, wanda hakan ya sa nasarar Afolabi ta zama babban abin tarihi a fannin ilimi.
Sakamakon dai shi ne na farko, tun da aka fara JAMB CBT a shekarar 2013.
Afolabi dan asalin jihar Ekiti, ana daukarsa a matsayin daya daga cikin hazikan dalibai a makarantar, ya kasance hazikin matashin dalibi ne mai tsananin kishirwar ilimi, ya zama abin alfahari da kwaikwayo ga sauran dalibai.
Afolabi Wanda dalibine na makarantar Icons Comprehensive College Ijapo Estate, Akure, jihar Ondo, ya samu wannan nasaran ce bisa sadaukarwarsa da da'arsa, da bajintar karatunsa.
Article Translation in English Language.
Afolabi Olumide Ayodeji became the best student of all the students to get the most marks in the 2025 JAMB entrance examination where he got a total of 370 marks.
The student received the following points in the subjects:
Mathematics – 98
Physics - 98
Chemistry – 94
English. - 80.
JAMB has confirmed that no candidate has scored 370 marks since 2013, making Afolabi's achievement a historic achievement in the field of education.
The result is the first since JAMB CBT started in 2013.
Afolabi, a native of Ekiti state, is regarded as one of the brightest students in the school, he is a brilliant young student with a great thirst for knowledge, he became a source of pride and example for other students.
Afolabi, a student of Icons Comprehensive College, Ijapo Estate, Akure, Ondo State, has achieved this achievement because of his dedication, ethics, and academic prowess.
0 Comments:
Post a Comment