Fittaciyar jarumar kannywood Saratu Gidado wacce aka fi sani da daso ta rasu yau Talata bayan ta kwanta barci bayan tayi sahur din azumi na 30 Kamar yadda 'yan uwanta suka sanar da manema labarai. ta rasu tana da shekaru 56 a duniya.
Za'a yi jana'izarta yau Talata da misalin Karfe 4:00pm a birnin Kano.
Daso wacce yawanci tafi fitowa a matsayin mace mai fada da jaraba ta Fara harkan fina-finai tun a shekaran 2000, shekaru 24 da suka gabata, ta kasance hazika a fannin wacce ba za'a manta da irin gudunmawar da ta bayar a harkan fina-finan Hausa ba.
FIM din ta na farko shine Linzami da wuta wanda Kamfanin shirya fina-finan Hausa na Sarauniya ya shirya.
0 Comments:
Post a Comment