Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar Lahadi, ya kai ziyarar ban-girma ga Sarkin Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a fadarsa da ke Oke-Aremo, cikin birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ziyarar ta kasance ne domin ƙarfafa dangantaka da daɗaɗɗen zumuncin dake tsakanin al'ummar Hausawa da Yarbawa, tare da inganta haɗin kai tsakanin al'ummomin biyu.
Sarkin Kano ya isa fadar Olubadan tare da tawagar mabiyansa, inda aka tarbe shi cikin girmamawa.
A yayin ziyarar, Sanusi ya bayyana farin cikinsa da sake ziyartar fadar, yana mai cewa birnin Ibadan tamkar gida na biyu ne a gare shi.
Ya bayyana cewa yana da kyakkyawar dangantaka da al'ummar Ibadan tun kafin ya zama Sarkin Kano, inda ya jaddada cewa ya daÉ—e yana hulÉ—a da mutanen birnin.
Bayan isar tawagar Sarkin Kano, sarakunan biyu sun gudanar da ganawar sirri a wani sashe na cikin fadar kafin daga bisani su fito zuwa babban É—akin taro domin yi wa sauran mahalarta jawabi.
Ana kallon wannan ziyara a matsayin wata muhimmiyar dama ta ƙarfafa dangantakar tarihi, al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummar Arewa da Kudu maso Yammacin Najeriya.
Jaridar The PUNCH ta rawaito cewa ziyarar ta samo asali ne daga kyakkyawar dangantaka da aka daÉ—e ana yi tsakanin al'ummomin Hausawa da Yarbawa.
Ana sa ran samun ƙarin bayanai game da ziyarar da tattaunawar da sarakunan biyu suka gudanar.
Tags
Labarai
