Wata kotu a ƙasar Philippines ta bayar da sammacin kama fitaccen malamin addini, Apollo Quiboloy, wanda ke tsare a gidan yari, kuma hukumomin Amurka ke nema bisa zargin safarar yara domin lalata da su da wasu laifuffuka.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani babban ci gaba da zai iya share fagen mika shi ga hukumomin Amurka domin fuskantar shari'a kan zarge-zargen da ake yi masa.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Shari'a ta Philippines, Polo Martinez, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Kotun Yankin Makati ta bayar da sammacin kama Quiboloy da kuma umarnin hana shi fita daga ƙasar a ranar Alhamis.
Ya ce kotun ta dauki matakin ne bayan ta gano hujjojin farko da ke nuna yiwuwar aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su.
Gwamnatin Philippines ta shigar da bukatar mika Quiboloy ga Amurka a wata kotun ƙasa a ranar Litinin, watanni uku bayan gwamnatin Amurka ta gabatar da bukatar a hukumance a watan Agusta.
A karkashin dokokin Philippines, yanzu kotun za ta gudanar da zaman sauraron shari'a kafin yanke hukuncin ko za a mika shi ga Amurka ko a'a.
Haka kuma, umarnin kotun ya shafi wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin, wato Teresita Dandan da Helen Panilag, wadanda ke cikin shugabannin cocin Kingdom of Jesus Christ (KOJC) da Quiboloy ke jagoranta.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu matan biyu ba su shiga hannun jami'an tsaro ba.
A wani bangare kuma, fadar shugaban ƙasar Philippines ta musanta rade-radin cewa an bayar da sammacin kama faston ne domin ya yi daidai da ziyarar da Shugaban Amurka, Donald Trump, zai kai birnin Manila a ranar 17 ga watan Nuwamba domin halartar taron ƙungiyar ƙasashen kudu maso gabashin Asiya (ASEAN).
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar, Claire Castro, ta bayyana cewa daidaituwar lokacin kawai ta faru ne bisa sa'a.
Quiboloy, wanda ke kiran kansa da suna "zaɓaɓɓen ɗan Allah", yana tsare ba tare da beli ba, yayin da yake fuskantar shari'ar safarar mutane a birnin Pasig.
Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.
Haka kuma, yana fuskantar wata shari'a daban kan zargin cin zarafin yara a birnin Quezon City.
Sai dai Quiboloy ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa, inda ya bayyana cewa bai aikata laifukan ba.
Zarge-Zargen da Amurka Ke Yi Masa
A shekarar 2021, wata babbar kotun shari'ar manyan laifuffuka a Amurka ta tuhumi Quiboloy kan zargin hada baki wajen safarar mutane domin lalata da su ta hanyar tilastawa, yaudara da amfani da karfin iko.
Sauran tuhume-tuhumen sun hada da safarar yara domin lalata da su da kuma safarar makudan kudade ba bisa ka'ida ba.
Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta kuma danganta wasu daga cikin shugabannin cocinsa da zargin gudanar da ayyukan da suka saba doka.
A cewar bayanan binciken 'yan sanda, wasu daga cikin wadanda ake zargin an yi wa amfani da su sun fuskanci barazana da yaudara ta hanyar amfani da koyarwar addini domin tilasta musu aikata abubuwan da ba su so.
Rahotanni sun ce an yi wa wasu barazanar cewa za a same su da azabar Allah ko kuma wasu halittun mutuwa idan suka tona asirin abubuwan da suka faru.
Sai dai a lokacin, cocin ya bayyana cewa mambobinsa suna da 'yancin zabar abin da suke so.
Kungiyar addinin Quiboloy ta yi ikirarin cewa tana da miliyoyin mabiya, sannan tana da gidan talabijin da ke gudanar da shirye-shirye a Philippines.
Quiboloy na da kusanci da tsohon shugaban ƙasar Philippines, Rodrigo Duterte.
Duk da kasancewarsa a tsare, ya tsaya takarar kujerar Sanata a zaben shekarar da ta gabata, inda ya samu kuri'u kusan miliyan 5.6, amma bai yi nasarar lashe kujerar ba.
Matakin da kotun ta dauka yanzu na iya kara dagula matsalolin shari'ar da Quiboloy ke fuskanta, yayin da hukumomin Philippines ke nazarin bukatar Amurka ta mika shi domin fuskantar tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tags
Labarai
