Katsina Ta Yaye Jami’an Tsaron Dazuzzuka 1,008 Domin Ƙarfafa Yaƙi da Rashin Tsaro

Katsina Ta Yaye Jami’an Tsaron Dazuzzuka 1,008 Domin Ƙarfafa Yaƙi da Rashin Tsaro

Gwamnatin Jihar Katsina ta yaye jami’an tsaron dazuzzuka 1,008 da aka horas domin kare dazuzzuka da kuma yaƙi da ayyukan ’yan bindiga, masu tayar da ƙayar baya da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin jihar.

An kafa rundunar ne bisa haɗin gwiwar gwamnatin jihar da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsaro da hana miyagu amfani da dazuzzuka a matsayin mafaka.

Da yake jawabi yayin bikin yaye jami’an, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa kafa rundunar wani shiri ne na Gwamnatin Tarayya domin ƙarfafa yaƙin da ake yi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ribadu, wanda wani darakta a ofishinsa mai suna I. O. Shotaye ya wakilta, ya bayyana cewa jami’an sun kammala horo na tsawon makonni takwas, wanda hukumomin tsaro daban-daban suka gudanar.

Ya kuma bayyana cewa cikin jami’an 1,008 da suka kammala horon, mata 18 ne.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Umaru Dikko Radda, ya gode wa Gwamnatin Tarayya bisa amincewa da kafa rundunar, yana mai cewa za ta taimaka wajen ƙarfafa matakan tsaron da gwamnatin jihar ke ɗauka domin kawo ƙarshen rashin tsaro.

Gwamnan ya ce jami’an za su haɗa kai da sauran jami’an tsaron al’umma da ke aiki a jihar domin inganta sa ido, kare dazuzzuka da kuma dakile ayyukan miyagu.

Ya kuma tabbatar wa jami’an cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa musu da dukkan kayan aiki da sauran buƙatun da za su taimaka musu wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Radda ya bayyana kyakkyawan fata cewa kafa rundunar za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar, yana mai cewa an samu ci gaba mai kyau a fannin tsaro a cikin 'yan shekarun nan.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu babu wata babbar hanya ko kasuwa da aka rufe a jihar sakamakon matsalar rashin tsaro, yana mai cewa hakan na nuna irin ci gaban da aka samu a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.

Ana sa ran kammala horon jami’an tsaron dazuzzuka 1,008 zai ƙara ƙarfafa ayyukan tsaro, musamman a yankunan da ke makwabtaka da dazuzzuka, waɗanda suka sha fama da hare-haren ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Ahmad B Sani

Manufarmu ita ce samar da sahihan labarai da muhimman bayanai kan al'amuran yau da kullum cikin harshen Hausa da Turanci, domin wayar da kan al'umma da isar da sahihan bayanai ga duniya.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form